Wani bincike ya gano asusu 890 a bankin Switzerland Credit Suisse da ake zargin suna da alaƙa da ’yan Nazi, a cewar Sanatan Amurka Chuck Grassley, gabanin zaman sauraron Majalisar Shari’a ta Majalisar Dattawan Amurka ranar Talata. Grassley ya ce asusun sun haɗa da wasu na lokacin Yaƙin Duniya na Biyu da ba a taɓa bayyana ba, ciki har da na Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus, kamfanin kera makamai, da kungiyar Red Cross ta Jamus.
Sanatan ya ce rahotannin binciken sun nuna cewa alaƙar bankin da ƙungiyar SS ta Nazi ta fi zurfi fiye da yadda aka sani a baya, inda reshen tattalin arzikin SS ya riƙe asusu a Credit Suisse. Har ila yau, an gano sabbin bayanai kan wani tsari da aka yi amfani da shi wajen taimaka wa ’yan Nazi tserewa zuwa Argentina bayan yaƙi.
Bankin UBS, wanda ya sayi Credit Suisse a 2023, ya ce yana aiki tare da tsohon mai gabatar da ƙara na Amurka, Neil Barofsky, domin kammala binciken. UBS da Credit Suisse sun bayyana nadama kan rawar da bankunan Switzerland suka taka a wancan lokaci, suna mai cewa an riga an cimma yarjejeniyar duniya a 1999 don rufe ƙorafe-ƙorafen Holocaust.
Shugaban UBS a Amurka, Robert Karofsky, ya ce bankin ya ɗauki alhakin ci gaba da binciken da gaske domin fitar da cikakken rahoto na ƙarshe. Ya jaddada cewa burin su shi ne bayyana gaskiya ga duniya game da abin da ya faru a wannan “duhun shafi” na tarihin bankunan Switzerland.
Majiyar Labari: REUTERS

















