Wata babbar kotu a Abuja ta tuhumi tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami, da laifukan da suka shafi ta’addanci da kuma almundahanar kuɗi.
Ana zargin Malami da “sanin” taimakawa ɗaukar nauyin ta’addanci ta hanyar gaza gurfanar da wasu mutane da ake zargi da hakan duk da rahotannin da suka kai ofishinsa, tare da tuhume shi da ɗansa Abdulaziz da mallakar bindiga da harsasai ba tare da lasisi ba. Dukansu sun musanta zarge-zargen.
Tun da farko, hukumomi sun tuhumi Malami, matarsa da ɗansa da laifin halatta kuɗaɗen haram da suka kai Naira biliyan 8.7, inda aka ba shi beli a watan da ya gabata kafin a sake kama shi jim kaɗan bayan haka.
Shari’ar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro da ta’addanci da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40,000 da kuma raba kusan miliyan biyu da muhallansu, lamarin da ya sanya shari’ar Malami ta ja hankalin jama’a.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














