Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin gaggawa bayan mummunan harin da aka kai a ƙauyen Worro da Nuku na ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda aka kashe mutane da dama. Lamarin ya tayar da hankula a fadin kasar, inda shugaban ya jaddada kudurinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce an tura sabuwar bataliyar soji ƙarƙashin Operation Savannah Shield, domin daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomin da ke cikin hadari. Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin, yana bayyana maharan a matsayin marasa tausayi da suka kai hari kan fararen hula.
Shugaban ya kuma nuna takaicinsa kan yadda aka kashe mutanen da suka ƙi amincewa da tilasta musu wata tsattsauran aƙida, yana yabawa al’ummar yankin da suka zaɓi Musulunci mai zaman lafiya. Ya bukaci haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar da hukunta masu laifi.
Rahotanni sun ce an kashe fiye da mutum 160, yayin da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar da mutuwar mutum 75 a ziyararsa fadar sarkin Kaiama. Ana zargin maharan sun fito ne daga gandun dajin Kainji da ke jihar Neja. Jihar Kwara na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a ‘yan kwanakin nan.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














