Aljeriya ta fara, a karon farko, wasu ayyukan tsabtace muhalli a ɗaya daga cikin wuraren da Faransa ta gudanar da gwaje-gwajen nukiliya a hamadar Sahara a shekarun 1960. Kamfanin dillancin labarai na gwamnati APS ya ce an ƙaddamar da aikin ne a ranar tunawa da gwaje-gwajen, waɗanda suka bar gurɓata muhalli da matsalolin lafiya ga mazauna yankin.
Rahotanni sun nuna cewa Faransa ta gudanar da aƙalla gwaje-gwajen nukiliya 17 a Sahara tsakanin 1960 da 1966. Aljeriya na kallon gwaje-gwajen a matsayin laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama. Aikin tsabtacewar na gudana ne da albarkatun cikin gida, musamman a wurin Taourirt Tan Afella – In Ekker da ke lardin Tamanrasset.
Wani shirin bidiyo na Ma’aikatar Tsaro ya bayyana cewa yankin ya fuskanci fashewar karkashin ƙasa mai ƙarfi sosai, tare da malalar iskar radiyo da ta yi illa ga muhalli. Har yanzu ana gano sinadarai masu radiyo kamar Cesium-137 da plutonium, lamarin da ya sa aka fara aikin bayan cikakken nazarin haɗarin lafiya da muhalli.
Hukumomi sun ce sansanin “tsabtacewar ɓangare” da aka kafa zai zama misali ga sauran wuraren gwaji. An tura na’urori na musamman domin tattara da adana sharar nukiliya a kwantena na kankare. Sai dai rashin taswirori da bayanan fasaha daga Faransa na ci gaba da kawo cikas wajen gano dukkan yankunan da gurɓata ta shafa.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














