Gwamnatin New Zealand ta sanar da kakaba takunkumi da hana zirga-zirga ga wasu manyan jami’an Iran, bisa zargin take haƙƙin ɗan adam da kisan fararen hula yayin zanga-zangar da aka yi a ƙasar. Ministan harkokin wajen ƙasar, Winston Peters, ya ce matakin ya shafi mutum 40, ciki har da ministan cikin gida Eskandar Momeni, ministan leƙen asiri Esmail Khatib da babban lauyan ƙasa Mohammad Movahedi-Azad. An kuma ambaci mambobin rundunar IRGC cikin waɗanda aka sanya wa takunkumin.
Peters ya jaddada cewa ’yan Iran na da haƙƙin yin zanga-zanga cikin lumana da ’yancin faɗar albarkacin baki, yana mai cewa an take waɗannan haƙƙoƙi. Ya ƙara da cewa New Zealand ta bi sahun Australia, Amurka, Birtaniya, Kanada da Tarayyar Turai wajen ɗaukar matakan. Duk wanda ya shiga jerin hana zirga-zirgar ba zai iya shiga ko wucewa ta New Zealand ba.
Wellington ta riga ta ɗauki irin waɗannan matakai a baya, inda aka hana wasu jami’an Iran 55 zirga-zirga. Haka kuma, New Zealand ta kakaba takunkumi kan ’yan Iran 29 da cibiyoyi 19 bisa zargin tallafa wa Rasha a yaƙin Ukraine.
A gefe guda, wani rahoto daga ofishin shugaban ƙasar Iran ya lissafa kusan mutum 3,000 da suka mutu a rikicin zanga-zangar da ta ɓarke a ƙarshen 2025, yana mai cewa fararen hula da jami’an tsaro na cikin waɗanda suka rasa rayukansu. Zanga-zangar ta samo asali ne daga matsin tattalin arziki, yayin da Iran ke zargin ƙasashen waje da ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.














