Nijeriya

INEC ta canza ranakun zaɓen 2027 saboda watan Ramadan

INEC ta matsar da zaɓen 2027 gaba don kauce wa faɗawa cikin watan Ramadan.

Newstimehub

Newstimehub

27 Feb, 2026

34c25465179d4b838caf81137c7db05f2cb0a86d912649b1a984b2e110d86944

Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (INEC) ta sauya jadawalin zaɓen 2027 bayan korafe-korafen da Musulmai suka yi kan yadda ranakun da aka fara sanyawa suka yi daidai da watan azumin Ramadan da kuma kusa da ƙaramar Sallah. Masu ruwa da tsaki sun nuna cewa hakan na iya rage yawan fitowar masu kaɗa ƙuri’a.

A baya, an saka 20 ga Fabrairu 2027 don zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, sai 6 ga Maris don na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi. Daga bisani majalisar dattawa ta gyara dokar zaɓe, inda ta rage wa’adin sanar da zaɓe daga kwanaki 360 zuwa 300, abin da ya bai wa INEC damar sauya ranakun.

Sabon jadawalin ya nuna cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun tarayya ranar 16 ga Janairu 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi zai gudana 6 ga Fabrairu 2027. Haka kuma an fitar da sabbin ranakun kamfe, zaɓen fid da gwani da sanar da sunayen ‘yan takara.

INEC ta ce sauyin na da nufin tabbatar da sahihin shiri da bai wa ‘yan ƙasa damar gudanar da ibadarsu ba tare da tangarda ba.

Majiyar Labari: TRT HAUSA