Shugaba Donald Trump ya yi Allah wadai da Iran bayan ta ƙaryata cewa tana tattaunawa da Amurka, inda ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na intanet cikin fushi cewa dakarun Amurka za su ci gaba da rufe mashigar Hormuz har sai Tehran ta ƙulla “yarjejeniya, ko kuma miƙa wuya gaba daya.”
Trump ya ce Iran tana yin “fuska biyu” saboda “fito wa fili da kuma nuna isa” da ta yi kan cewa ba wata yarjejeniya tsakaninta da Amurka.
A saƙon da ya wallafa a ranar Litinin a shafin sada zumunta na Truth Social, Trump ya bayyana cewa “Ko Iran ta yarda ko ba ta yarda ba, muna tattaunawa game da mafita ga wata matsala da ta haifar na tsawon shekaru da dama.”
Saƙon nasa ya zo ne bayan da Iran ta ce babu wata tattaunawa ta kai-tsaye da take yi da Washington, kamar yadda Trump ya dage cewa za su sabuwar tattaunawa lokacin da ya dakatar da barazanar kai hari kan Iran a ƙarshen makon jiya.
A ranar Litinin, Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce tattaunawarta da Oman kawai take yi don shirye-shiryen raba iko kan gudanar da Mashigar Hormuz, hanya mai muhimmanci ga cinikin makamashi na duniya.
Trump ya dage cewa Iran ce ta nemi a tattauna – “wasu za su ce ‘roko ta yi'” – amma yanzu tana wani “shaci-faɗi” game da gudanar da Hormuz.
Trump ya dage cewa, “Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka ce take riƙe da ikon Hormuz baki ɗaya da kuma ‘Tsaronmu’ ko kuma, kamar yadda wasu ke cewa, ‘Katangar Ƙarfe ta Amurka!’ Babu abin da zai shiga Iran, sai dai idan mun so, kuma babu abin da zai shiga sai dai idan an cim ma yarjejeniya, ko kuma an miƙa wuya gaba ɗaya.”
Tun a ranar 28 ga Fabrairu Trump ya ƙaddamar da yaƙi tare da Isra’ila kan Iran.
Kuma manufofin farko na Amurka sun haɗa da lalata nukiliya da makamai masu linzami na Iran.
Fiye da watanni biyar bayan haka, Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage sama marasa matuƙa a kan sansanonin Amurka da ƙawayenta a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma ta ci gaba da adana tarin uranium ɗinta masu yawa.
Duk da matsin lambar Amurka, hare-haren Iran kan jiragen ruwa a Hormuz sun yi mummunan tasiri ga cinikin makamashi a duniya, wanda hakan ya bai wa Tehran sabuwar dama mai ƙarfi a rikicin.
















