Qatar ta ce tawagarta da ke shiga tsakani ta shafe kusan makonni biyu tana musayar ra’ayoyi da nufin sake farfaɗo da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.
“Mun shafe kusan makonni biyu muna musayar ra’ayoyi daban-daban kan sake farfaɗo da tattaunawa tsakanin Washington da Tehran,” in ji kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Majed al-Ansari, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na Qatar suka rawaito.
Ƙasar Qatar da Pakistan, sun jima suna shiga tsakanin ɓangarorin biyu.
“Muna aiki ta hanyar tawagarmu da ke shiga tsakanin Tehran da Washington don ganin ko za a ci gaba da tattaunawar, kuma a halin yanzu suna tafiya tsakanin manyan biranen daban-daban da fatan samun ci gaba a wannan hanya,” in ji al-Ansari.
Ya ƙara da cewa Qatar ta samu tabbaci daga jami’an gwamnatin Amurka cewa Washington na son cim ma yarjejeniya da Tehran.
Al-Ansari ya ce akwai buƙatar a samar da “mafita ta yankin da za ta cim ma daidaito da kuma fahimtar duniya wadda za ta kare hanyoyin ruwa kamar Mashigar Hormuz.”
“Miƙa hanyoyin ruwa ga ikon mallakar ƙasa ɗaya da amfani da su a matsayin makami zai kafa tarihi mai haɗari ga dukkanmu,” in ji shi.
Amurka ta kai hare-haren soji a wurare da dama a Iran a kwanan nan a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan rashin jituwa kan hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin hanyoyin samar da makamashi da cinikayyar duniya mafi muhimmanci a duniya, duk da yarjejeniyar fahimtar juna da ɓangarorin biyu suka sanya wa hannu a tsakiyar watan Yuni.
Iran ta mayar da martani da hare-hare kan abin da ta ce cibiyoyin sojin Amurka ne da kayan aikinsu a ƙasashen Larabawa, ciki har da Saudiyya.
Wasu daga cikin hare-haren sun jawo asarar rayuka da kuma lalata kayayyakin more rayuwa na fararen-hula, lamarin da ya jawo suka daga ƙasashen da abin ya shafa kuma kira kan a dakatar da su.
“Ƙaruwar hare-hare na ba-zata“
Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da yaƙi da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 3,000, a cewar Tehran.
Iran ta mayar da martani da hare-haren wadda ta ce sun kashe Amurkawa da Isra’ila.
Kalaman Qatar sun zo ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar da gargaɗin tsaro a ranar Lahadi tana mai cewa “sakamakon tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, yanayin tsaro ya kasance mai sarkakiya, tare da karuwar hare-hare na ba-zata.”
Ta bukaci ‘yan Amurka a yankin da su yi taka-tsantsan, wadanda kuma ke kusa ko wajen yankin da su sa ido sosai.
Ofishin jakadancin Amurka da dama a yankin, ciki har da na Hadaddiyar Daular Larabawa da Iraki da kuma Jordan, sun fitar da irin wannan gargaɗin a ranar Lahadi.
Yayin da yake bayyana yadda zai tunkari yakin, a safiyar ranar shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News cewa “Tambayata ita ce, shin yaushe ne zan rusa ƙasar gaba daya? Ya kamata su mayar da hankali.”
Trump ya bayyana zabin da ke gabansa a halin yanzu a matsayin ko dai ya rusa kasar gaba daya, ko ya bar ta ta “durkushe” ta fuskar tattalin arziki, ko kuma a cim ma yarjejeniya da ita; inda ya kara da cewa “za a ga manyan abubuwa nan ba da jimawa ba.”

















