Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya, National Bureau of Statistics, ta bayyana cewa ƙasar ta tara kusan naira tiriliyan 2.28 na harajin VAT a watanni uku na ƙarshen shekarar 2025.
Rahoton da hukumar ta fitar a ranar 3 ga Maris ya nuna cewa adadin ya ƙaru da kashi 10.66 idan aka kwatanta da watanni uku na baya, inda aka tara tiriliyan 2.06.
Rahoton ya nuna cewa mafi yawan kudaden sun fito ne daga VAT na cikin gida wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.12. Sauran kudaden sun hada da biliyan 680 daga VAT na kayayyaki da ayyuka daga ƙasashen waje, da kuma kusan biliyan 479.79 daga harajin shigo da kaya.
Haka kuma an nuna cewa idan aka kwatanta da irin wannan lokaci na shekarar 2024, kudaden harajin VAT da aka tattara sun karu da kashi 28.10 cikin dari, wanda ke nuna karuwar kudaden shiga daga haraji a Nijeriya.














