Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin fitar da kudi nan-take domin gyara kayayyakin aikin sararin samaniyar Nijeriya bisa tsarin da aka shimfiɗa na inganta sararin samaniyar ƙasar.
Shugaban Bola Tinubu ya umarci a fitar da kuɗi nan take domin inganta kayayyakin aikin sararin samaniyar Nigeria, a wani bangare na sabon shirin shekara 25 da gwamnati ta tsara domin bunƙasa fannin. Shugaban ya ce za a tura buƙatar kuɗin zuwa Majalisar Zartarwar Tarayya domin ta duba tare da amincewa da aiwatar da shirin.
Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta tsaya tana kallon ci gaban fasahar sararin samaniya a duniya ba, sai dai za ta shiga cikin gasar domin cin gajiyar damar da ke tattare da shi. A cewarsa, zuba jari a wannan fanni zai taimaka wajen inganta noma, bincike, tsaro, sadarwa da kuma tattalin arzikin intanet.
Shugaban ya kara da cewa tattalin arzikin sararin samaniya na kara habaka a duniya kuma ana hasashen zai kai darajar dala tiriliyan daya nan da shekarar 2040. Don haka gwamnati na ganin cewa saka jari a wannan fanni zai taimaka wa Nijeriya wajen bunkasa fasaha, kare muhalli da kuma inganta tsare-tsaren gargadi game da bala’o’i kamar ambaliyar ruwa da gobara.














