Gwamnatin Mali ta sake jaddada goyon bayanta ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan rasuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei. Firaministan Mali, Abdoulaye Maïga, ya kai ziyara ofishin jakadancin Iran da ke Bamako domin sanya hannu a littafin ta’aziyya da aka buɗe domin girmama marigayin.
Maïga ya bayyana cewa ya wakilci shugaban gwamnatin rikon kwarya na Mali, Assimi Goïta, da gwamnatin kasar da al’ummarta wajen isar da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Iran da jama’arta. A cikin sakon da ya rubuta, ya yaba da rawar da Khamenei ya taka, yana mai cewa ya mutu yana kare muradun kasar Iran da jama’arta har zuwa numfashinsa na ƙarshe.
Ya kara da cewa mutuwar Khamenei ta bar babban gibi, amma gadonsa a matsayin jagora da hangen nesansa na duniya mai adalci da mutunta ikon kasashe za su ci gaba da kasancewa a cikin tarihin masu fafutukar kare ‘yancin kasashensu.
Bikin sanya hannu a littafin ta’aziyyar ya gudana ne tare da halartar jakadan Iran a Mali da ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, inda hukumomin kasar suka kuma yi addu’ar samun rahama ga marigayin da sauran wadanda suka rasa rayukansu.














