Gwamnatin Nijeriya ta bukaci hukumomin Mozambique da su gaggauta sakin ’yan kasarta 42 da aka ruwaito cewa an kama ba tare da bayyana wani laifi da suka aikata ba. Shugabar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce wannan mataki abin damuwa ne kuma yana iya nuna wariya ga ’yan Nijeriya.
A cewarta, idan har akwai laifin da suka aikata, ya kamata a gurfanar da su a gaban kotu maimakon tsare su ba tare da bayani ba. Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen ne yayin wani samame da aka kai a kasuwar kayan ababen hawa, inda aka kama ’yan Nijeriya kawai yayin da aka bar sauran ’yan kasuwar kasashe daban-daban.
Hukumar NiDCOM ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka tsare sun jikkata yayin kamen, an kwashe musu kayayyakinsu, kuma wasu sun kamu da rashin lafiya a gidan yari. Saboda haka ta bukaci gwamnatin Mozambique ta tabbatar da lafiyarsu tare da warware lamarin cikin gaggawa.














