Gabas Ta Tsakiya Nijeriya

Nijeriya Ta Fara Kwashen ‘Yan Kasarta Daga Iran

Nijeriya ta fara kwashe ‘yan kasarta daga Iran ta hanyar kan iyakar Armenia yayin da rikicin yankin ke kara tsananta. Armike ta bayanna cewa babu dan Nijeriya dan ya mutu har iya yanzu.

Newstimehub

Newstimehub

11 Mar, 2026

aa559303a21e627d3477e856cab1e82d27e76ed62b83c3e5b10a53d226228f4c

Gwamnatin Nijeriya ta fara kwashe ‘yan kasarta daga Iran sakamakon rikicin da ke kara tsananta tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila. Shugabar Hukumar ‘Yan Nijeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce jami’an ofishin jakadancin Nijeriya na raka ‘yan kasar da ke son barin Iran zuwa kan iyakar Armenia domin su tsallaka cikin aminci.

A cewarta, jami’an Nijeriya na jiran ‘yan kasar a kan iyaka domin tarbar su, tare da taimaka musu su koma gida lafiya. Ta kuma tabbatar da cewa ba a samu rahoton mutuwar wani dan Nijeriya ba sakamakon rikicin da ke gudana a Iran.

Matakin kwashe ‘yan Nijeriyar na zuwa ne yayin da rikicin da ya barke kwanaki goma sha daya da suka wuce ya riga ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 1,300 a Iran, yayin da dubban wasu suka jikkata ko suka rasa muhallansu.

Majiyar Labari: TRT HAUSA