Direbobi a babban birnin Mali, Bamako, na fuskantar matsalar ƙarancin man gas bayan da kamfanin makamashi na ƙasar ya fara amfani da mafi yawan man domin rage yawan katsewar lantarki.
Ƙungiyar kamfanonin man ƙasar ta bayyana a ranar Talata cewa wannan mataki ya sa wasu gidajen mai suka fara rasa man gas, abin da ya jawo cinkoso a gidajen mai. Mali, wadda ba ta da teku, na dogaro ne da shigo da man fetur ta manyan motocin dakon mai. Amma a watannin baya-bayan nan an samu tangarda wajen isar da man saboda hare-haren ‘yan ta’adda kan jerin motocin dakon mai.
Tun daga watan Satumba, wasu ‘yan ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda ke ƙoƙarin gurgunta tattalin arzikin ƙasar ta hanyar hana shigowar mai, inda suka kai hare-hare kan tankokin mai tare da toshe muhimman hanyoyin shiga Bamako.
Ko da yake an samu ƙarin man fetur tun watan Disamba wanda ya taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziki, a yanzu man gas ya fara ƙarewa a wasu gidajen mai a Bamako. Rahotanni sun nuna cewa a ranar Talata an ga dogayen layuka na motoci a gidajen mai, yayin da wasu motocin dakon yashi da duwatsu suka daina aiki saboda rashin man gas.
Matsalar ta kuma shafi harkokin sufuri, inda kafofin watsa labarai suka ce sama da motoci 100 masu jigilar fasinjoji sun tsaya aiki a Bamako ranar Litinin. Rahotanni sun ce ana ba kamfanin makamashin ƙasar EDM fifiko wajen samun man gas domin samar da wutar lantarki, musamman yayin da ake fama da tsananin zafi.
A gefe guda kuma, wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta ce a ƙarshen watan Janairu wasu ‘yan ta’adda sun kashe direbobin manyan motoci 10 da matasa biyu a kusa da iyakar Senegal.














