Wasu manyan sassan makami mai linzami daga Iran sun fadi a safiyar Laraba kusa da wani kauye a yankin Damascus na kasar Syria bayan sojojin Isra’ila sun kakkabe makamin a sararin samaniya. Tashar talabijin ta Syria, Alikhbaria Syria TV, ta ce tarkacen makamin ya sauka ne a kusa da kauyen Ma’as da ke yankin karkarar Damascus.
Rahoton ya ce duk da girman tarkacen makamin da ya fadi, ba a samu wata barna ko jikkata ba. Sai dai lamarin ya haifar da firgici tsakanin mazauna yankin da ke kusa da wurin.
Wani mazaunin kauyen Al-Mushaqaq mai suna Ibrahim Al-Mousa ya shaida cewa lokacin da aka kakkabe makamin a sararin samaniya, mutane da dama sun firgita, musamman yara. Ya kara da cewa da tarkacen ya fadi kan wani gida, zai iya haddasa mummunar barna.
A kwanakin baya ma an ruwaito irin wadannan lamura a kudancin Syria, musamman a lardunan Daraa da Quneitra, inda tarkacen makamai da aka kakkabe ke fadowa a kasa. Wannan na faruwa ne a yayin da rikici ke kara tsananta bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya jawo mutuwar sama da mutane 1,200.
Bayan hare-haren, Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren drones da makamai masu linzami kan Isra’ila, Jordan, Iraq da kuma wasu kasashen Gulf da ke dauke da sansanonin sojin Amurka.














