Senegal ta sanar da cewa za ta ɗaukaka ƙara bayan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta kwace mata kambin AFCON tare da bai wa Maroko nasara da ci 3-0. Wannan hukunci ya zo ne watanni biyu bayan wasan ƙarshe da aka buga a Rabat, wanda ya cika da ruɗani da cece-kuce.
A lokacin wasan, ‘yan wasan Senegal sun bar fili na ɗan lokaci domin nuna rashin amincewa da fanareti da aka ba Maroko a ƙarshe, kafin daga bisani su dawo su ci gaba da wasa. Duk da haka, CAF ta ce wannan mataki ya saba dokokin gasar, wanda ya sa aka ayyana Senegal a matsayin wadda ta yi watsi da wasan.
CAF ta yi amfani da dokokin AFCON da ke cewa duk ƙungiyar da ta bar wasa ba tare da izini ba za ta rasa shi da ci 3-0. Duk da cewa Senegal ta ci wasan a filin wasa da ci 1-0 a ƙarin lokaci, hukuncin ya sauya sakamakon gaba ɗaya, tare da bai wa Maroko kofin.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta soki wannan hukunci tana mai cewa ba adalci ba ne, tare da shirin kai ƙara zuwa kotun wasanni ta duniya (CAS). Rikicin ya samo asali ne daga bugun fanareti mai jayayya da aka ba Maroko, wanda mai tsaron ragar Senegal ya tare, kafin Senegal ta ci ƙwallon nasara daga baya.














