An fara aiwatar da sabuwar dokar Senegal bayan wallafa ta a jaridar gwamnati, wacce ta ƙara tsaurara hukunci kan hulɗar jinsi ɗaya. Dokar, wacce ‘yan majalisa 138 cikin 165 suka amince da ita, ta gyara sashe na dokar laifuka inda a baya ake bayar da hukuncin shekara 1 zuwa 5, amma yanzu an ƙara shi zuwa shekaru 5 zuwa 10 tare da tara mai yawa.
Sabuwar dokar ta fayyace abin da ake kira “aikin da ba na dabi’a ba” a matsayin hulɗar jinsi ɗaya ko wasu ayyukan jima’i da suka shafi gawa ko dabba, tare da ƙara hukunci ga waɗanda ke goyon baya ko tallafa wa irin waɗannan ayyuka, inda za su iya fuskantar ɗaurin shekaru 3 zuwa 7 da tara.
Dokar na zuwa ne a lokacin da aka riga aka kama mutane da dama tun farkon Fabrairu, inda aƙalla mutane 52 aka kama bisa zargin aikata irin waɗannan laifuka. Senegal na cikin ƙasashen Afirka da dama da ke da tsauraran dokoki kan hulɗar jinsi ɗaya, duk da cewa wasu ƙasashe sun sassauta ko ma sun soke irin waɗannan dokoki a shekarun baya.
Majiyar Labari: AA














