Ɓangarorin sojin ruwan na sojin Amurka da ake aiki a yankin mashigin ruwan Hormuz sun fuskanci harbin makamai masu linzamin Iran, bayan wani harin sojin Amurka kan wata tankar mai ta Iran, kamar yadda kafofin watsa labaran Iran suka ruwaito, suna masu ambato wani jami’ain sojin da ba a bayyana sunansa ba.
Lamarin ya tilasta wa jaragen ruwan na sojin Amurka jadabaya bayan hare-hare makamai masu linzamin Iran sun lalata sassansu, kamar yadda ta ruwaito daga farkon ranar Juma’a.
Babu tabbacin lokacin da lamarin ya auku.
Sojin Amurka sun ƙaddamar da hare-hare kan tashoshin jiragen ruwa na Qeshm da Bandar Abbas, kamar yadda wani wakilin kafar Fox News ya bayyana a shafin sada zumunta na X inda yake ambato wani babban jami’in Amurka.
Pentagon ba ta mayar da martani ba nan take ga buƙatar neman tsokaci kan lamarin ba, amma a ranar Laraba , sojin Amurka ta ce ta kassara wani jirgin jigilar mai mai ɗauke da tutar Iran da ke ƙoƙarin tafiya tashar jiragen ruwan Iran.
Sojin Amurka ta ce dakarun Amurka sun kai hari ƙasar wani jirgin jigilar ruwan da wani jirgin yaƙi samfurin F-18 .
Fashe fashen abubuwa kusa da Bandar Abbas da tsibirin Qeshm
Sai dai kuma, an ji ƙararraki masu kama da na fashe-fashen abubuwa kusa da Bandar Abbas da tsibirin Qeshm, kamar yadda kafafen watsa labaran Iran suka bayyana.
Kamfanin dillancin labaran Fars News Agency da ƙasar ke da ƙwarya ƙwaryar iko a kai ya ba da rahoton cewa mazauna wurin sun ji ƙararraki na fashewar abubuwa kusa da Bandar Abbas, yana mai ƙarawa da cewa ta yiwu an kai hari wani ɓangare na Bahman Pier yayin musayar wutan tsakanin dakarun Iran da “dakarun abokan gaba.”
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya tabbatar da fashe-fashen abubuwan a yankin, yana mai nuna cewa za su iya kasancewa suna da nasaba da gargaɗin rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC) ga jiragen ruwan da ke aiki a mashigin ruwan Hormuz.
A wani lamarin na daban kuma, kafar watsa labarai mallakar ƙasar Iran IRIB ta ba da rahoton fashewar wani abu a wata gada a tsibirin Qeshm, tana mai cewa har yanzu ana bincike game da lamarin.
Sauran kafafan watsa labaran Iran kuma sun ba da rahoton fashe-fashen abubuwan, yayin da sojin Isra’ila ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ita “ba ta da da masaniya game da irin wannan” harin.
Kamfanin dillancin labaran Mizan ya ce ƙarrarkin fashe-fashen abubuwan da aka ji a Qeshm sun faru ne sakamakon yadda tsarin tsaron sararin samaniyar ke kakkaɓo ƙananan jiragen mara matuƙa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya ba da rahoton cewa tsarin tsaron sararin samaniya sun kakkaɓo jirage mara matuƙa biyu a Bandar Abbas.














