Ghana ta yi sanar a ranar Talata cewa za ta kwashe ‘yan ƙasarta 300 daga Afirka ta Kudu, bayan an samu ƙaruwar tashe-tashen hankula masu alaƙa da ƙin jinin baƙi a faɗin ƙasar a ‘yan makonnin nan.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ministan harkokin wajen ƙasar Samuel Okudzeto Ablakwa ya ce Shugaba John Dramani Mahama ya amince da aikin kwashe mutanen.
“Waɗannan ‘yan Ghana da suke cikin ƙunci sun bi shawarar ma’aikatar harkokin waje daga farko kuma sun yi rajista da ofishin jakadancinmu a Pretoria domina a ceto su bayan hare-haren ƙin jin baƙi na baya bayan nan,” kamar yadda ya rubuta.
“Gwamtatin ƙasar Ghana za ta ci gaba da kare lafiyar dukkan ‘yan Ghana a gida da ƙetare.”
Zanga-zangar ƙin jinin baƙi
Matakin ya biyo bayan jerin zanga-zangar ƙin jin baƙi ne a Afirka ta Kudu, tare da iƙirarin hare-hare da tsangwama kan sauran ‘yan ƙasashen Afirka.
Nijeriya da Ghana sun nuna damuwarsu game da lamarin.
Sai dai kuma gwamnatin ƙasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da dukkan iƙirarin ƙin jinin baƙi.
“‘Yan Afirka ta Kudu ba sa ƙin jinin baƙi,” kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasar Vincent Magwenya ya shaida wa manema labarai a makon da ya gabata.
“Abin da ake samu shi ne ‘yar zanga-zanga a nan da can, wadda ta halasta a ƙarƙashin tsarin mulkinmu.”
Magwenya ya ce Afirka na buƙatar magance rikici da rashin zaman lafiya da kuma “mulki mara kyau” da ke janyo yawan ci-rani a faɗin nahiyar.
An kira jakada
A ƙarshen watan da ya gabata, gwamnatin da ke Accra ta kira jakadan Afirka ta Kudu domin nuna rashin jin daɗi kan lamuran ƙin jinin baƙi da suka auku a kan ‘yan Ghana.
Afirka ta Kudu ita ce ƙasa mai tattalin arziƙi mafi ƙarfi a Afirka kuma gida ce ga fiye da baƙi miliyan uku ko kuma kashi biyar cikin 100 na adadin mutanen ƙasar.
Amma rashin aikinyi ya kai kashi 30 cikin 100, lamarin da ke ruruta tashin hankali da ma’aikata ‘yan ci-rani.
A tashin hankali mafi muni a kan baƙi a cikin shekaru 20 da suka gabata, an kashe mutum 62 a shekarar 2008. An kuma samu arangama na tashin hankali a shekarun 2015 da 2016 da 2019.














