A yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar Nijar, sojojin kasar sun sake sanar da wata babbar nasara kan kungiyoyin masu tayar da kayar baya. Hare-haren da aka kai a wurare daban-daban sun nuna yadda ake kara kaimi wajen murkushe ta’addanci.
Sanarwar da Cibiyar Hadin Gwiwar Ayyuka ta Sojojin Nijar (CICO) ta fitar, wadda aka karanto a gidan talabijin na gwamnati, ta ce dakarun kasa tare da goyon bayan hare-haren jiragen sama sun hallaka ‘yan ta’adda 43 tare da kama mutum 28 da ake zargi da taimaka musu.
Haka kuma, an kwace makamai da harsasai masu yawa, ciki har da nakiyoyi 5,452, wayoyin tayar da nakiya 68, fiye da lita 68,000 na kayan fashewa da dubban kwayoyi masu illa da ake zargin an shirya kai wa kungiyoyin masu laifi.
Tun daga shekarar 2015, Nijar na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda musamman a yankin Diffa da ke iyaka da Nijeriya inda Boko Haram ke kai hare-hare, da kuma yankunan Tahoua, Dosso da Tillabéri da ake danganta hare-harensu da kungiyar Islamic State (Daesh).
Kungiyar ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai ranar 29 ga Janairu kan filin jirgin saman Diori Hamani International Airport da ke Yamai, babban birnin Nijar.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














