Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawa da Iran na tafiya “da kyau” kuma za ta iya samar da sakamako cikin ƙarshen mako nan.
“Na ji cewa tattaunawar kanta na tafiya da kyau, haƙiƙa,” kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai, yana mai ƙarawa da cewa akwai yiwuwar cim ma yarjejeniya: “za ta iya faruwa … zuwa ƙarshen mako.”
Tunanin Trump game da lamarin ya sha bamban da na Ministan Harkokin Wajen Iran , Abbas Araghchi, wanda ya ce har yanzu hanyar tattunawa da Amurka a buɗe take, amma “ba a samu wani takamaiman ci-gaba” ba a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin na Gabas Ta Tsakiya.
Trump ya kuma ce yana son ya raba tattaunawar Amurka da Iran da tattaunawar da ake yi game yaƙin Isra’ila da Hezbollah a Lebanon.
“Zan so na raba su, Zan so na samu wani abu daban, saboda wani abu ne daban,” in ji Trump.
“A karon farko mun yi tattaunawa da Hezbollah,” kamar yadda shugaban Amurka ya bayyana game da ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon.
“Sun amince jiya cewa ba za su yi harbi ba, Isra’ila ba za ta yi harbi ba , za mu zuba ido mu gani,” in ji Trump .
An yi ƙasa-ƙasa da maganar musayar wuta
A cikin dare Amurka ta ce ta kakkaɓo jirage mara matuƙa na Iran kuma ta kai hari kan wata cibiyar bayar da umarni ta Iran ta ƙasa, yayin da dakarun Iran suke ƙaddamar da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami a ƙasashen Larabawa na gaɓar Tekun Fasha masu maƙwabtaka.
Trump ya yi ƙasa-ƙasa da musayar wutar, yana mai cewa : “Wani ɓangare daban ne na duniya, ka sani . Zan iya cewa a wancan ɓangaren na duniya, tsagaita wuta shi ne idan kana harbi a wani yanayi matsakaici.”
“Duk abin da ya faru yana da dalili, mun kai musu hari sosai a daren jiya, a jiya da daddare ma mun kai musu hari,” kamar yadda Trump ya bayyana game da Iraniyawa, yana mai ƙarawa da cewa: “Da aka yi mini bayani, na ce babu matsala .'”
Wata yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran ta fara aiki tun farkon watan Afrilu , inda yarjejeniyar Lebanon ta fara aiki a tsakiyar wata.
Duk da haka, an ci gaba da arangama tsakanin ɓangarorin da ke cikin rikicin.
















