Wani sanatan Amurka, Mark Warner, ya yi gargaɗi kan ƙaruwar wariyar addini da tashin hankalin ƙiyayya a ƙasar, yana zargin gwamnatin Donald Trump da taka rawa wajen yaɗa ƙyamar Musulunci da ra’ayin ƙin Larabawa.
Da yake jawabi a Majalisar Dattawa, Warner ya ce al’ummomin Musulmai da Larabawa na fuskantar nuna bambanci mai tsanani, yana misalta kalaman da Trump ya taɓa yi kan ‘yan asalin Somali, wanda ya kira “masu ƙazanta” tare da cewa ba a son su a Amurka.
Sanatan ya kuma yi Allah wadai da wasu maganganu a Majalisar da suka bayyana Musulunci a matsayin “addini mai guba,” yana mai kira ga jami’an gwamnati da su tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin al’ummomi, musamman yayin da watan Ramadan ke gabatowa.














