Kasar Botswana ta sanar da shirin buɗe ofishin jakadancinta a Moscow tare da gayyatar masu zuba jari na Rasha su shiga haɗin gwiwa kan ma’adanan rare earths da harkar lu’ulu’u, a cewar ministan harkokin wajen ƙasar.
Botswana ta bayyana cewa tsayin daka kan zaman lafiya da kwanciyar tattalin arzikinta ya sanya ƙasar ta zama wuri mai kyau ga jarin Rasha. Rasha kuma na ci gaba da ƙarfafa tasirinta a Afirka yayin takun siyasa da kasashen Yammacin Duniya. A halin yanzu, lu’ulu’u na samar da kusan rabin kudaden waje da kuma kaso mai tsoka na kudaden shiga na Botswana.














