Afirka

Mali ta haramta hawa babura a wajen birane saboda hare-haren ta’addanci

Kazalika hukumomin ƙasar sun sanar da dakatar da “shigo da kayayyaki, da zirga-zirga jama’a, tallacde-tallace, da kuma rabon kyautar babura” a dukkan fadin kasar.

Newstimehub

Newstimehub

4 Jun, 2026

7d62b1ee55f094c8b87561f3c29c0f947bf5b8d11f5ce0fe9973d09439381ba5

Gwamnatin ƙasar Mali ta haramta amfani da wasu irin babura a wajen manyan birane a ƙasar, matakin ya zo ne yayin da kasar ke fafatawa da kungiyoyin ‘yan ta’adda, kamar yadda kafar yada labarai na gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Laraba.

Kungiyoyin ‘yanta’adda sun fi yawan amfani da babura wajen kai hare-hare a Mali.

Umarnin dokar wadda aka karanto ta gidan talabjin din gwamnatin ƙasar a yammacin Laraba ta ce ‘‘ an dakatar da zirga-zirga da babura masu karfin injin 125cc ko fiye da haka, a wajen manyan biranen ƙasar nan.’’

Ko ya dake dokar ba ta shafi babban birnin Bamako, manyan biranen yankin da wasu yankunan birane.

Dakatar da shigo da kayayyaki

Kazalika hukumomin ƙasar sun sanar da dakatar da “shigo da kayayyaki, da zirga-zirga jama’a, tallace-tallace,da kuma rabon kyautar babura” a dukkan faɗin kasar.

Mali na fustantar tarin matsaloli na tsaro bayan hare-haren da ‘yanta’adda da ‘yan awaren Tuareg ke jagoranta suka kai ƙasar a ranakun 25 da 26 ga watan Afrilu inda suka kashe ministan tsaron ƙasar Sadio Camara a gidansa.

‘Yanta’addan sun toshe hanyoyi da dama da ake shiga Bamako tun daga ranar 30 ga Afrilu, inda suka kona motoci da dama da kuma manyan motocin daukar kaya.

Kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace yankuna da dama a arewacin ƙasar, ciki har da garin Kidal mai matukar muhimmanci.