Nijeriya

Majalisar dattawa ta Nijeriya ta nemi a kamo tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, kan tiriliyan N210

Wannan umarni ya biyo bayan ƙauracewa binciken da Mele Kyari ya yi akai-akai, wanda aka shirya don yin tambayoyi da Ofishin Babban Mai Binciken Asusun Gwamnatin Tarayya ya bijiro da su game da bayanan kuɗin kamfanin.

Newstimehub

Newstimehub

11 Jun, 2026

images 20 1

Ranar Larabar nan, Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya kan asusun gwamnati ya ba da umarnin kamo tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, saboda rashin bayyana gaban sa kan zargin da ya shafi wasu kuɗaɗe har Naira triliyan 210 da ba a san inda suke ba tsakanin shekarar 2017 da 2023.

Wannan umarni ya biyo bayan ƙaurace wa binciken da Kyari ya yi akai-akai, wanda aka shirya domin bincikar wasu tambayoyi da Ofishin Babban Mai Binciken Asusun Gwamnatin Tarayya ya bijiro da su game da bayanan kuɗin kamfanin a lokacin da ake bincikewa.

Sai dai, tsohon Babban Jami’in Kuɗi na NNPCL, Umar Isa, ya ƙalubalanci waɗannan zarge-zargen a gaban kwamitin, inda ya jaddada cewa babu wani kuɗi da ya ɓata, sannan ya bayyana adadin kuɗin na Naira tiriliyan 210 a matsayin abin da ke yaudarar mutane idan aka kwatanta shi da ainihin abin da kamfanin ya samu a wannan lokacin.

An ba da umarnin kama Mele Kyari ne bayan da ’yanmajalisar suka yanke shawarar kada su sake jinkirta binciken.

Yayin zaman, Sanatoci kamar Saliu Mustapha (daga Kwara ta Tsakiya), da Tony Nwoye (daga Anambra ta Arewa), sun yi kira da a kwantar da hankali, inda suka buƙaci kwamitin da ya sake ba Kyari wata damar daban domin ya bayyana, tare da bayanin cewa an ba da rahoton cewa ba shi da lafiya kuma yana karɓar magani a ƙasar Jamus.

Amma sauran mambobin kwamitin sun nuna adawa mai ƙarfi ga wannan buƙata, inda suka nace cewa dole ne binciken ya ci gaba ba tare da wani jinkiri ba, kuma suka buƙaci a fitar da takardar umarnin kama shi.

Sanata Abdul Ningi (daga Bauchi ta Tsakiya) ya bayyana cewa bai kamata a amshi uzuri na baki ba, ba tare da takardar shaida ta likita da ke nuna rashin lafiya ba. Daga baya Sanata Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya) ya goyi bayan wannan ra’ayi, kuma shi ne ma ya gabatar da ƙudurin neman kama Kyari a hukumance.

Yayin da yake goyon bayan ƙudurin, Mataimakin Shugaban kwamitin, Sanata Peter Nwaebonyi (mai wakiltar Ebonyi ta Arewa), ya yi gargaɗin cewa ƙara jinkiri zai rage darajar aikin kwamitin.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na tara da wannan kwamiti ke zama kan tambayoyi 19 da Ofishin Babban Mai Duba Asusun Gwamnatin Tarayya ya gabatar ga NNPCL, ya kuma ce guda uku daga ciki su ne na jagoranci zaman.

“Ya Shugaban Majalisa, lokacin da za a ba da umarnin kama Mele Kyari shi ne yanzu, domin kwamitin nan ya kamata ya kammala aikin da aka ba shi kuma ya miƙa rahoto ga Majalisar Dattijai.”

Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya kuma bayyana cewa Majalisar Dattijai na fuskantar barazanar rage ikon da take da shi idan har ta gaza tilasta bin sammacin da take bayarwa.

“Wasu mutane sun yi imanin cewa sun fi ƙarfin Nijeriya. Dokar dole ne ta yi aiki don kama zaki, ba wai sai lokacin kama zomo kaɗai ba,” in ji shi.

Bayan kaɗa ƙuri’a ta baki, Shugaban Kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo (mai wakiltar Gombe ta Arewa), ya yanke hukuncin cewa kamata ya yi a kama Kyari kuma a kawo shi gaban kwamitin.

“Duk inda Mele Kyari yake, a kamo shi a kawo shi gaban wannan kwamiti,” in Sanata Dankwambo.

A tsakiyar wannan ce-ce-ku-ce akwai zargin cewa ba a san inda Naira triliyan 210 suke ba a cikin asusun NNPCL. Amma Isa ya yi watsi da wannan iƙirari, inda ya ce hakan bai zo daidai da lissafi da bayanan kuɗi na kamfanin ba.

Ya ce, ”Da a ce kuɗi sun ɓace a NNPC lokacin da muke kan mulki, da ba za mu sami ƙwarin-gwiwar wallafa bayanai a asusun binciken kuɗi na kamfanin ba. Fiye da shekaru 40, waɗannan bayanan ko sau ɗaya ba a shirya su ba, ba a bayyana su ga jama’a ba, kuma ba a taɓa mika su ga Babban Mai Duba Asusun Gwamnati ba.

“Kuɗi Naira tiriliyan 210 adadi ne mai yawan gaske. Jimillar kuɗaɗen shiga na NNPCL a lokacin da ake bincikawa ya kai kusan Naira tiriliyan 54.5, tun ma kafin a cire kuɗaɗen da aka kashe wajen samar da man. Ba zai taɓa yiwuwa a ce Naira tiriliyan 210 sun ɓace ko ba a san inda suke ba,” in ji shi.

Ya kuma yi watsi da iƙirarin cewa an kashe Naira biliyan 5.8 wajen yi wa kamfanin NNPC Limited rijista, inda ya bayyana zargin a matsayin mara tushe kuma mai cutarwa. Sannan ya buƙaci kwamitin da ya tantance alƙaluman daga hukumomin da abin ya shafa.