Rundunar ’yansandan Jihar Legas ta fara ɗaukar matakin doka kan wasu zarge-zarge masu nauyi da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta gayyaci wani fitaccen fasto domin amsa tambayoyi.
’Yansandan Jihar Legas da ke kudu maso-yammacin Nijeriya sun gayyaci Fasto Chris Okafor, babban fasto na cocin Mountain of Liberation and Miracles Ministries, bisa zarge-zargen aikata fyaɗe a lokuta daban-daban.
A wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, Abimbola Adebisi, ta fitar ranar Lahadi da daddare, ta ce an umarci faston ya gabatar da kansa a gaban Sashen Binciken Laifuka na Jiha (SCID), Panti, ranar Litinin da ƙafin ƙarfe 10:00 na safe domin amsa tambayoyi.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yansanda na Jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yansanda mai kula da SCID da ya gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen manyan laifuka da ake yi wa faston. Rundunar ta tabbatar da cewa an miƙa takardar gayyata ga Okafor ta hannun lauyansa, tare da sa ran zai bayar da cikakken haɗin kai ga masu bincike.
Haka kuma, Kwamishinan ’Yansandan ya ba da umarni a samar da tsaro ga mutanen da aka ce an ci zarafinsu, domin su iya zuwa su bayar da bayanai ba tare da tsoro ba. Rundunar ta jaddada cewa za a kiyaye sirrin duk wanda abin ya shafa da shaidu, tare da kare su bisa doka.
’Yansandan sun yi kira ga duk wanda abin ya shafa ko ke da sahihan bayanai da shaidu da su tuntuɓi SCID kai-tsaye ko Sashen Hulɗa da Jama’a na rundunar. Jimoh ya nanata cewa rundunar na bin ƙa’idojin ƙwarewa, gaskiya da adalci, yana mai cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.
Binciken ya biyo bayan zarge-zargen da suka bayyana a shafukan sada zumunta a watan Disamban 2025, ciki har da ikirarin da jarumar Nollywood Doris Ogala ta yi a wasu bidiyoyin Instagram, inda ta ce ta shafe shekaru tana hulɗa da faston, tana kuma zarginsa da cin zarafi da karya alƙawura.














