Gabas Ta Tsakiya

Iran za ta gudanar da jana’izar Jagoran Addini da aka kashe Ali Khamenei a ranakun 4-9 ga Yuli

Za a yi ban kwana da Ali Khamenei a babban birnin Iran a ranar 4-5 ga Yuli, inda aka shirya binne shi a ranar 9 ga Yuli a Mashhad, a cewar rahotannin kafofin watsa labaran Iran.

Newstimehub

Newstimehub

13 Jun, 2026

2026 06 13t124114z 857365408 rc21pla4qwim rtrmadp 3 iran crisis khamenei funeral

Iran za ta gudanar da tsarin jana’izar Jagoran Addinin Ƙasar da aka kashe Ali Khamenei tsakanin 4 zuwa 9 ga Yuli, a cewar rahotannin kafar watsa labarai ta gwamnatin Iran.

Shirin zai ƙunshi bankwana a Tehran a ranar 6 ga Yuli da kuma a Qom ranar 7 ga watan na Yuli.

A ranar 9 ga Yuli kuma za a binne Khamenei a hubbaren Imam Reza a birnin Mashhad bayan gudanar da al’amuran jana’iza a ranar 8 ga Yuli.

Hare-haren Isra’ila da Amurka ne waɗanda aka fara kai su ranar 28 ga Fabrairu ne suka yi ajalinsa. Hare-haren sun kuma yi ajalin manya kwamandojin soji da dama da jami’an gwamnati.

Pakistan ta shiga tsakani inda aka tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu, kuma tun daga nan aka ci gaba da yunƙurin cim ma yarjejeniya mai faɗi.