Yawaitar tashe-tashen hankula da kuma gaza hukunta ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai na ci gaba da tauye ’yancin addini a Nijeriya, in ji babbar ƙwararriyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan ‘yancin addini a ranar Jumma’a, tana mai ƙarawa da cewa ana iya fahimtar dalilin da ya sa wasu waɗanda abin ya shafa ke bayyana lamarin a matsayin tsanantawa ko ma kisan kare-dangi.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Nazila Ghanea, wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Imani, bayan wata ziyarar bincike ta makonni biyu da ta kai Nijeriya.
Kalaman nata sun zo ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya a bara lokacin da ya yi Allah wadai da abin da ya kira “kisan kare dangi” na Kiristoci a ƙasar.
Nijeriya, wadda kusan ta kasu tsakanin Arewa mai rinjayen Musulmi da Kudu mai rinjayen Kiristoci, na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da dama.
Waɗannan sun haɗa da ta’addancin da ya daɗe yana addabar Arewa, ayyukan ƙungiyoyin masu laifi masu ɗauke da makamai, da kuma rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake yawan samu a yankin Tsakiyar Nijeriya mai mabanbantan addinai.
A cewar Ghanea, raunin aiwatar da doka da rashin hukunta masu laifi na sa hare-hare da ramuwar gayya tsakanin al’ummomi su ci gaba ba tare da shamaki ba.
Kalaman Trump kan zargin kisan kare-dangi na Kiristoci sun haifar da ɗan tangarɗa a dangantaka tsakanin Amurka da Nijeriya, duk da cewa daga baya ƙasashen biyu sun ƙarfafa haɗin gwiwa ta fuskar soja wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.
Da aka tambaye ta kai tsaye game da zargin Trump, Ghanea ta ce ta tuntubi manyan masana shari’a.
“Sun ce mini, ‘Ba zan iya cewa babu wani wuri a Nijeriya da ake samun kisan kare-dangi ba,’” in ji ta inda take nakalto abin da suka gaya mata.
“Sai dai a gefe guda,” ta ƙara da cewa tana yin nazari kan abin da ta gano, “shin mun ga wani umarni kai tsaye daga gwamnati da nufin hallaka wata al’ummar addini ko wata? Ban ga hakan ba.”
Ana sa ran Ghanea za ta gabatar da cikakken rahoto kan binciken da ta gudanar ga Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a wani lokaci nan gaba.

















