Norway ta samu kai wa zagayen ‘yan-16 a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026 da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico, bayan doke Ivory Coast a wasansu na safiyar Talata.
Erling Haaland ne ya ci ƙwallo ana saura minti huɗu a tashi wasa, wanda ta bai wa Norway nasara da ci 2-1 kan Ivory Coast a wasansu na zagayen ‘yan-32.
Ƙwallon da Haaland ya ci ita ce ƙwallo ta biyar da ya zura a gasar zuwa yanzu.
Tun da fari, abokin wasansa, Antonio Nusa ya zura ƙwallo ta farko ga Norway ana minti shida kafin hutun rabin lokaci.
Kafin ƙwallon Haaland, ɗanwasan Ivory Coast, Amad Diallo ya rama ƙwallon farkon a minti na 74, wanda ta bai wa ƙasarsa fata har zuwa dab da ƙarshen wasan.
A zagayen sili-ɗaya-ƙwale na ‘yan-16, Norway za ta kara da Brazil a birnin New York na Amurka ranar Lahadi mai zuwa.

















