Nijeriya

INEC ta kara wa ma’aikatanta albashi da alawus-alawus na gudanar da ayyukan zabe a Nijeriya

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar na shiyyar Arewa ta Tsakiya domin tantance shirye-shiryen gudanar da zaɓen.

Newstimehub

Newstimehub

7 Nov, 2026

16631db1 19e1 4bbc b537 a1fac9482d59 1794037789144

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta amince da sabon tsarin albashi ga ma’aikatanta, tare da ƙara alawus-alawus na gudanar da ayyukan zaɓe da kuma kuɗaɗen tafiyar da ayyukan ofisoshinta na jihohi da kashi 150 cikin 100, a wani ɓangare na shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar na shiyyar Arewa ta Tsakiya domin tantance shirye-shiryen gudanar da zaɓen.

Amupitan ya ce an ɗauki matakan ne domin inganta jin daɗin ma’aikata, ƙarfafa ayyukan zaɓe da kuma tabbatar da gudanar da zaɓe cikin inganci, wanda zai shafi fiye da masu rajistar katin zaɓe miliyan 103 a rumfunan zaɓe 176,846 a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa sabon tsarin albashin ma’aikatan hukumar, mai suna Consolidated Election Management Body Salary Structure (CEMBSS), wanda aka ƙirƙira bayan hukumar ta fice daga tsarin albashin ma’aikatan gwamnati na yau da kullum, ya fara aiki tun ranar 1 ga Janairun 2026.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da kammala matakan samar da kuɗaɗen aiwatar da sabon tsarin albashin.

Hukumar ta kuma amince da ƙarin albashi da alawus-alawus na haɗari da gudanar da ayyukan zaɓe ga ma’aikatanta, yayin da kuɗaɗen gudanar da ofisoshinta na jihohi suka ƙaru da kashi 150 cikin 100 tun daga ranar 1 ga Yulin 2026.

Dangane da kayan aiki, Amupitan ya ce an raba motocin ɗaukar kaya da na gudanar da ayyuka ga ofisoshin hukumar na jihohi da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar, yayin da aka sayo sababbin motoci ƙirar SUV guda 20 domin kwamishinonin zaɓe na jihohi.

Ya ƙara da cewa sakatarorin gudanarwa na hukumar su ma za su samu sababbin motoci domin ƙarfafa ayyukan hukumar.

Sai dai shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikatan cewa dole ne bayan inganta jin daɗinsu ya kasance suna bin da rashin nuna bambanci na siyasa da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Ya umarci ma’aikatan hukumar da su dakatar da tafiya hutun shekara, tare da gargaɗin cewa sakaci, rashin zuwa aiki, nuna goyon baya ga ‘yan siyasa ko wani ɓangare da almundahana da kuɗaɗe za su jawo musu hukunci na ladabtarwa.

Amupitan ya kuma umarci kwamishinonin zaɓe na jihohi da sakatarorin gudanarwa da su ƙarfafa sa ido kan halartar ma’aikata da kuma tabbatar da ɗaukar alhaki, yana mai cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani hali da zai iya kawo cikas ga sahihanci da amincin zaɓen 2027 ba.