Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) sun ba ’yan Nijeriya haƙuri kan ci gaba da samun matsalar katsewar wuta a sassan ƙasar, inda suka amince da irin wahalhalun da jama’a ke fuskanta sakamakon ƙarancin wutar lantarki da aka shafe makonni ana fama da shi.
Babban Darakta kuma Shugaba na Ƙungiyar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (ANED), Sunday Oduntan, ne ya ba da haƙurin a ranar Litinin, yayin wata hira da ya yi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.
“Da farko, ina so in fara da ba ’yan Nijeriya haƙuri. Ya zama wajibi mu ba da haƙuri, domin ’yan Nijeriya sun shafe makonni suna fuskantar wannan matsala,” in ji shi.
Da yake magana a shirin, Oduntan ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin komawar masu ruwa da tsaki a ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya ga ɗora wa juna laifi. Ya tuna da irin wannan takaddama da ta gudana tsakanin 2016 da 2019.
Ya ce a baya, kamfanonin rarraba wutar lantarki, masu kula da layukan isar da wuta, kamfanonin samar da wuta da masu samar da iskar gas sun sha ɗora wa juna alhakin ƙarancin wutar lantarki, maimakon haɗa kai domin magance matsalolin da ke haddasa hakan.
“Babbar matsalarmu ita ce mun sake komawa kan wannan mummunar hanya da muka bi tsakanin 2016 da 2019. Wace hanya ce? Ɗora wa juna laifi,” in ji shi.
Oduntan ya bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki sun zargi Kamfanin Isar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), yayin da masu kula da isar da wutar suka ɗora laifin kan kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos). Su kuma kamfanonin samar da wutar sun nuna masu samar da iskar gas da matsalolin biyan kuɗi a matsayin sanadin matsalar.
Ya yi gargaɗin cewa sake barkewar irin wannan rashin jituwa zai ƙara dagula ƙoƙarin warware matsalolin wutar lantarkin ƙasar.
Shugaban ANED ɗin ya kuma yi tambayoyi kan bayanan da Kamfanin Gudanar da Tsarin Wutar Lantarki Mai Zaman Kansa na Nijeriya (NISO) da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) suka fitar game da musabbabin ƙarancin wutar.
A cewarsa, NISO ya danganta matsalar samar da wutar lantarki, a wani ɓangare, da ƙarancin ruwa a madatsun ruwa da kuma rashin isasshen iskar gas. Sai dai daga baya NNPC ya fitar da sanarwar da ke nuna cewa akwai iskar gas.
Sai dai Oduntan ya nuna shakku kan bayanin NNPC, yana mai cewa ya kamata kamfanin ya fayyace ko akwai bashin kuɗin da ba a biya ba wanda ke kawo cikas ga samar da iskar gas ga kamfanonin samar da wutar lantarki.
“Daga sanarwar NNPC, a bayyane yake cewa sun zo ne suka gaya mana rabin gaskiya. Abin da nake tsammanin NNPC ya kamata ta yi shi ne ta gaya mana ko akwai matsalar biyan kuɗi. Muna bukatar mu san ko an biya kuɗin iskar gas kuma an kai shi, wa ya biya, wa kuma bai biya ba,” in ji shi.
Ya yi kira ga Ministan Wutar Lantarki da ya jagoranci haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki domin gano ainihin musabbabin ƙarancin wutar lantarkin da kuma samar da mafita mai ɗorewa.
Oduntan ya ce ci gaba da musayar zarge-zarge tsakanin masu samar da iskar gas, NNPC, TCN da NISO ba zai magance matsalar ba, matuƙar babu ingantaccen jagoranci da haɗin kai.
Dogon Lokaci Ba Tare da Wuta ba
Haƙurin ya zo ne a daidai lokacin da fushin jama’a ke ƙaruwa kan ƙarancin wutar lantarki, yayin da gidaje da ’yan kasuwa ke fama da matsalar katsewar wuta na tsawon lokaci a makonnin baya-bayan nan.
Matsalar ta kuma sake haifar da tambayoyi kan ingancin tsarin rarraba masu amfani da wutar lantarki zuwa rukunan Band A, B da C a Nijeriya. Wannan tsarin ne ke ƙayyade kuɗin wutar da kwastomomi za su biya bisa mafi ƙarancin adadin sa’o’in da ake sa ran za su samu wuta.
Masu amfani da wutar lantarki, ciki har da waɗanda ke ƙarƙashin rukunin Band A, waɗanda ake sa ran za su samu aƙalla sa’o’i 20 na wuta a kullum, na ci gaba da korafi kan rashin isasshen wutar.
Tsananin zafin da ake fama da shi a lokacin rani ya ƙara ta’azzara matsalar, inda mazauna yankuna da dama ke fama da rashin wutar da za su yi amfani da fanka da na’urorin sanyaya iska.
Matsalar katsewar wutar ta janyo zanga-zangar jama’a da kuma suka daga fitattun ’yan Nijeriya.

















