Jadawalin wasannin quarter-final na Gasar Cin Kofin Afrika ta CAF AFCON 2025 da ake gudanarwa a Maroko ya kammala bayan samun nasarar Algeria a zagaye na 16 kan DR Congo da ci 1–0 bayan karin lokaci. Wannan nasara ta tabbatar wa Algeria gurbi a matakin ’yan takwas tare da shirya fafatawa da Najeriya, wadda ta doke Mozambique da ci 4–0 domin tsallakewa matakin gaba.
Kafin wannan lokaci, kungiyoyin Senegal, Mali, Maroko, Kamaru da Masar sun riga sun samu tikitin shiga quarter-final, yayin da Côte d’Ivoire ta zama ƙungiya ta ƙarshe da ta cika jerin bayan ta doke Burkina Faso da ci 3–0. Rahoton ya nuna cewa wasannin quarter-final za su gudana tsakanin 9 zuwa 10 ga Janairu, a manyan filayen wasan kwallon kafa da ke Tangier, Rabat, Agadir da Marrakech.
Takaitaccen Jerin Kungiyoyin da Suka Cancanci Quarter-Final:
Senegal • Mali • Morocco • Cameroon • Egypt • Nigeria • Algeria • Côte d’Ivoire
Jadawalin Wasannin Quarter-Final (Kammalalle):
Mali vs Senegal – Juma’a, 9 Janairu | Grand Stade de Tanger, Tangier | 5:00pm WAT
Cameroon vs Morocco – Juma’a, 9 Janairu | Prince Moulay Abdellah Stadium, Rabat | 9:00pm WAT
Egypt vs Côte d’Ivoire – Asabar, 10 Janairu | Stade Adrar, Agadir | 8:00pm WAT
Nigeria vs Algeria – Asabar, 10 Janairu | Stade de Marrakech, Marrakech | 5:00pm WAT














