Gabas Ta Tsakiya

Amurka da Isra’ila sun kai sababbin hare-hare a Iran

Isra’ila ta ayyana dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar bayan ta kai hari Iran a yayin da ake tsaka da tattaunawa da Amurka.

Newstimehub

Newstimehub

28 Feb, 2026

1772261564152 6ev4y ff53661ba02592569bf0016b87ede6021d456116cb8b64bb654e6249d0d145a7

Ministan Tsaron Isra’ila Israel Katz ranar Asabar ya ce ƙasarsa da haɗin gwiwar Amurka sun kai “hare-haren kandagarki” a Iran, saboda abin da ya kira barazanar da take yi ga tsaron ƙasarsu.

Kazalika Katz ya ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa baki ɗaya, sannan ya yi kira ga ‘yan ƙasar su bi umarnin rundunar soji ta Home Front Command wadda ke da alhakin kare fararen-hula.

“Ƙasar Isra’ila ta kai harin kandagarki a Iran. Ministan Tsaro Israel Katz ya ayyana dokar ta-baci ta musamman a duka ƙasar,” a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron ƙasar.

Ganau sun ce sun ji manyan ƙararraki na fashewar abubuwa a Tehran, inda hayaƙi ya mamaye sararin samaniya, ko da yake kawo yanzu Iran ba ta yi martani ba.

An ji ƙarar fashe-fashe a Isfahan, Qom, Karaj da Kermanshah, a cewar kamfanin dillanacin labarai na Fars News Agency.

Hare-haren na zuwa ne a yayin da ake tattaunawa tsakanin Amurka da Iran sakamakon zaman ɗarɗar kan shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.

Rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sanarwa inda ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi kaffa-kaffa, tana mai gargaɗi game da yiwuwar hare-hare na makamai masu linzami.