Hukumar Kula da Kare Bayanai ta Holland (AP) ta ɗauki mataki mai tsauri kan wasu ƙananan hukumomi bayan gano cewa sun gudanar da binciken sirri kan al’ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba. Matakin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna yadda aka tattara bayanai masu matuƙar sirri cikin ɓoye, abin da ya tayar da kura game da mutunta ‘yancin jama’a da amincewa da hukumomi.
A cewar gidan rediyon NOS, an ci tarar ƙananan hukumomi goma jumillar euro 250,000, bayan bincike ya nuna cewa tun a shekarar 2021 aka fara ba da umarnin gudanar da irin waɗannan nazarce-nazarce a asirce. Binciken ya samo asali ne daga fargabar tsattsauran ra’ayi da ya danganci Daesh da kuma yaƙin basasar Syria, inda aka ɗauki wani kamfani na waje don tattara bayanai kan al’ummomin Musulmai.
Rahotannin sun ƙunshi bayanai masu muhimmanci kamar addini, mazhabar Musulunci, sunaye, hotuna, bayanan iyali, da tsarin gudanar da masallatai, inda a wasu lokuta aka haɗa cikakkun bayanan mutane. Wasu daga cikin rahotannin ma an miƙa su ga ‘yan sanda, hukumar NCTV da Ma’aikatar Al’amuran Jama’a da Aikin Yi.
Shugaban AP, Aleid Wolfsen, ya ce ƙananan hukumomin ba su da hujjar tattara irin waɗannan bayanai, yana mai cewa an keta sirrin jama’a matuƙa kuma hakan ya lalata amincewar da ake da ita ga hukumomin. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Delft, Ede, Eindhoven, Haarlemmermeer, Hilversum, Huizen, Gooise Meren, Tilburg, Veenendaal da Zoetermeer. Hukumar ta ce laifin ya yi tsanani ne saboda ya shafi bayanan addini masu matuƙar muhimmanci, kuma tuni wasu hukumomin suka amince da laifin, inda birnin Delft ya nemi afuwa daga ƙungiyoyin Musulmai na cikin gari.
Majiyar Labari: TRT WORLD














