A ranar 7 ga watan Disamba, ƙasar Benin ta fuskanci wani mummunan yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi. Sun yi garkuwa da manyan hafsoshin soja guda biyu kafin a samu nasarar kuɓutar da su cikin dare ba tare da rauni ba. Sojojin ƙasar, tare da taimakon ƙasashen yankin, sun yi gaggawar dakile shirin tare da tarwatsa ‘yan tawayen, yayin da shugaban su ya tsere.
A yau Litinin, birnin Cotonou yana fara dawowa daidai. Makarantu da kasuwanni sun buɗe, hanyoyi sun koma aiki, duk da cunkoson mota a wasu wurare. Jama’a na nuna farin ciki da godiya ga sojoji saboda kare ƙasar da dawo da zaman lafiya.
Asali: Africa News














