Hukumomin Burkina Faso sun tabbatar da mutuwar tsohuwar minista, Yolande Viviane Compaoré, bayan da aka gano gawarta a gidanta a wani unguwa mai yawan jama’a a birnin Ouagadougou a ranar 10 ga Janairu. A cewar ofishin mai gabatar da ƙara, binciken farko ya nuna cewa an kai mata hari a cikin gidanta kafin daga bisani a kashe ta.
Mai gabatar da ƙara ya sanar da buɗe cikakken binciken shari’a domin gano waɗanda suka aikata laifin da kuma duk wasu da ka iya taimaka musu. An kuma yi kira ga jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen gano gaskiyar abin da ya faru, yayin da har yanzu ba a kama kowa ba.
Yolande Viviane Compaoré ta kasance fitacciyar ‘yar siyasa a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Blaise Compaoré (1987–2014), inda ta rike mukamai da dama da suka haɗa da gwamna, ‘yar majalisa, ministar sufuri da yawon buɗe ido, da kuma ministar haɗin kan yankuna. Ta kuma shugabanci kwamitin harkokin waje da tsaro na majalisar dokoki, tare da jagorantar ƙungiyar mata ‘yan majalisar ƙasashen Francophonie.
Mutuwar ta ta janyo alhini da tashin hankali a ƙasar, musamman ganin cewa kisan ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da tunawa da rikice-rikicen siyasar da suka haifar da kifar da Blaise Compaoré a shekarar 2014. Hukumomin Burkina Faso sun sha alwashin zakulo gaskiya tare da hukunta duk masu hannu a wannan kisan gilla.














