Wani jami’in hukumar shige da fice ta Amurka, Immigration and Customs Enforcement (ICE), ya harbe wata mata ‘yar ƙasar Amurka har lahira a wani unguwa na birnin. Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da gwamnatin Donald Trump ke ƙara tura jami’an tsaro domin aiwatar da tsauraran matakan shige da fice, abin da shugabannin jihar Minnesota da na birnin suka zarga da janyo rudani da tashin hankali.
Rahotanni sun ce kusan mutane 1,000 sun taru a gaban wani ginin gwamnatin tarayya da ke ɗauke da kotun shige da fice, inda suka yi zanga-zanga suna zargin jami’an tarayya da kisan kai. Wasu jami’an tsaro masu sanye da kayan kariya sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayakin mai sa hawaye da ƙwallan barkono. Hukumomin Trump sun bayyana harbin a matsayin kare kai, suna zargin matar da yunƙurin kai wa jami’an hari da mota, yayin da magajin garin Minneapolis, Jacob Frey, ya ƙaryata wannan ikirari bisa faifan bidiyon shaidu da ke nuna sabanin bayanin gwamnati.
Bidiyoyin da aka ɗauka sun nuna jami’an ICE suna kusantar motar matar, Renee Nicole Good mai shekara 37, inda yayin da take ƙoƙarin barin wurin, wani jami’i ya harbe ta har sau uku. Gwamnatin Trump ta ce jami’in ya ji tsoron rasa ransa, amma shugabannin Minnesota sun bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali, tare da buƙatar janye jami’an tarayya daga birnin. Gwamnan jihar, Tim Walz, ya saka rundunar National Guard cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da aka rufe makarantu na kwanaki biyu domin kauce wa tashin hankali.
Renee Nicole Good, wadda aka kashe, uwa ce mai ‘ya’ya uku. Majalisar birnin Minneapolis ta ce tana taimakon al’umma ne a lokacin da aka kashe ta. Lamarin ya ƙara fito da rarrabuwar kai a siyasar Amurka, inda magoya bayan Trump ke goyon bayan matakin jami’an tsaro, yayin da masu adawa ke zargin gwamnati da amfani da ƙarfi fiye da kima. Hukumar FBI da hukumomin jihar Minnesota sun fara bincike kan harbin.














