A wani sabon rikici da ke kara ɗaga zafin muhawara tsakanin Amurka da Tarayyar Turai, gwamnatin Amurka ta sanar da hana bayar da biza ga wasu manyan jami’ai daga Turai, tana zarginsu da matsa lamba kan kafafen sada zumunta na Amurka domin toshe ra’ayoyin da ba su goyon baya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta hana biza ga tsohon kwamishinan Tarayyar Turai da wasu mutane hudu, bisa zargin cewa suna ƙoƙarin tilasta wa kamfanonin sada zumunta na Amurka yin takunkumin ra’ayi. Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Thierry Breton, tsohon jami’in EU mai kula da fasahar sadarwa, wanda ya sha yin takaddama da attajiran fasaha irin su Elon Musk kan bin dokokin Tarayyar Turai.
Ma’aikatar ta bayyana Breton a matsayin daya daga cikin masu tsara Dokar Digital Services Act (DSA), wadda ke tilasta wa manyan kafafen sada zumunta bin ka’idojin tace bayanai da nuna gaskiya a Turai.
Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya yi Allah-wadai da matakin, yana mai cewa Turai ba za ta amince a dora mata dokoki daga waje ba. Ya jaddada cewa dokar DSA an kafa ta ne ta hanyar dimokuradiyya kuma ba ta shafi Amurka kai tsaye ba.
Breton dai ya soki matakin a shafinsa na X, inda ya kira shi “farautar mayu,” yana kwatanta shi da zamanin McCarthy a Amurka, yana mai cewa matsalar takunkumin ra’ayi ba ta inda wasu ke zargi take ba.
Amurka ta kara tsananta suka kan dokokin EU bayan da Tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin X mallakin Elon Musk saboda karya dokokin DSA. Haka kuma, wasu kungiyoyi da jami’ai daga Jamus, Birtaniya da Amurka da ke yaki da yada bayanan karya sun shiga cikin jerin wadanda aka hana biza.













