Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dakatar da aiwatar da bizar ƙaura ga ‘yan ƙasashe 75, matakin da ke nuna sabon yunƙurin Shugaba Donald Trump na takaita shigowar baki da ke neman zama a ƙasar.
Wani kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce an dakatar da sarrafa bizar ƙaura ga waɗannan ƙasashe ba tare da bayar da takamaiman lokacin dawo da aikin ba. Wannan na zuwa ne mako guda bayan Amurka ta sanar da ƙarin ƙa’idoji ga ‘yan Najeriya masu neman bizar yawon buɗe ido ko kasuwanci (B1/B2), inda za a bukaci su ajiye jinginar kuɗi har dala $15,000, matakin da zai fara aiki daga ranar 21 ga Janairu, 2026.
Bayanan da aka wallafa a shafin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Travel.State.Gov, sun nuna cewa biyan jinginar kuɗi ba ya nufin tabbas na samun biza, kuma kuɗin da aka biya ba tare da umarnin jami’in ofishin jakadanci ba ba za a mayar da shi ba.
Amurka ta bayyana cewa ana buƙatar irin wannan jingina daga wasu ƙasashe da ake kallon su a matsayin “masu haɗari,” domin ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta tantance masu neman biza. Daga cikin ƙasashen da abin ya shafa akwai 27 a Afirka ciki har da Najeriya, Ghana, Masar da Senegal; 22 a Asiya; takwas a Turai; 13 a Arewacin Amurka da Caribbean; uku a Kudancin Amurka; da ɗaya a Oceania.
Matakin na shafar dubban masu fatan ƙaura, kuma ya sake tayar da muhawara kan manufofin shige da ficen Amurka, yayin da jami’ai ke cewa ana yin hakan ne domin kare tsaron ƙasa da tabbatar da cikakken bincike kan masu nema.














