A safiyar Lahadi, mazauna ƙauyen Apakolu da ke lardin Ituri a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun wayi gari cikin tashin hankali, bayan wani mummunan hari da wasu ’yan bindiga suka kai musu. Harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, sannan an sace wasu mutane, lamarin da ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ƙamari a wannan yanki.
Rahoton cikin gida na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa akalla mutane 22 ne suka mutu a harin, yayin da shugabannin ƙungiyoyin farar hula a yankin suka ce adadin ya kai 25, ciki har da maza 15 da aka same su a kashe a cikin wani gida, da wasu bakwai da aka tsinci gawarwakin su a kan hanya. An danganta harin ga ƙungiyar ’yan ta’adda ta Allied Democratic Forces (ADF) da ke yawan kai hare-hare a gabashin ƙasar.
Rahoton ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asuba, inda aka kuma sace wasu mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba. Kwanaki biyu kafin haka, ADF sun sake kai hari a ƙauyen Kazaraho da ke kusa, inda suka yi artabu da sojoji da ’yan sa-kai.
A wani harin daban, jami’an yankin sun ce ’yan ADF sun farmaki ƙauyen Musengo a lardin North Kivu, inda suka ƙona gidaje, shaguna da wata cocin Katolika, tare da kashe sojojin Kongo biyu a lokacin da aka mayar da martani.
Sojojin Kongo tare da na Uganda na ci gaba da kai farmaki kan ADF, amma duk da haka hare-haren ƙungiyar na ci gaba, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a watan Nuwamba kaɗai sun kashe mutane 138 a gabashin ƙasar.














