Wani matashi mai suna Naveed Akram, mai shekaru 24, wanda ake zargi da kai hari a lokacin bikin Hanukkah a Bondi Beach, Sydney, ya bayyana a kotu karo na farko ta hanyar bidiyo. Rahotanni sun ce ya halarci zaman ne daga gidan yari na tsaro mai ƙarfi na Goulburn, inda ake tsare da shi.
Akram na fuskantar tuhume-tuhume 59, ciki har da kisan kai da laifukan da suka shafi ta’addanci. Ana zargin cewa shi ne ya kai harin ranar 14 ga Disamba 2025, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15 tare da jikkata wasu 42. A yayin harin, ‘yan sanda sun harbe mahaifinsa, Sajid Akram, wanda ya rasu a wurin.
Zaman kotun ya fi mayar da hankali kan batutuwan shari’a, inda alkalin ya tsawaita dokar da ke kare bayanan wasu daga cikin wadanda abin ya shafa. Lauyan da kotu ta naɗa wa Akram, Ben Archibold, ya nemi karin lokaci domin tattaunawa da wanda yake karewa, yana mai cewa har yanzu ba a mika cikakken fayil din hujjoji ba.
Lauyan ya shaida wa manema labarai cewa shari’ar na iya ɗaukar lokaci mai tsawo, mai yiwuwa har zuwa shekarar 2027. Ya kara da cewa a halin yanzu ba zai iya bayyana matsayar kariya ba har sai an samu cikakken bayanin shari’ar.
Majiyar Labari: AA









