Burundi ta sake buɗe iyakarta ta ƙasa da Democratic Republic of Congo a ranar Litinin, bayan fiye da watanni biyu na rufewa sakamakon rikice-rikice a gabashin Congo. An buɗe mashigar Kavimvira–Gatumba Border, wadda ke da muhimmanci ga kasuwanci da zirga-zirgar jama’a zuwa Bujumbura.
Gwamnan South Kivu ya ce an buɗe iyakar da safe, yayin da hotuna a kafafen sada zumunta suka nuna matafiya da ‘yan kasuwa suna jerin gwano domin kammala tantancewa. An rufe iyakar ne tun Disamba bayan ƙungiyar ‘yan tawaye M23ta kwace Uvira, kafin daga bisani su janye a Janairu.
Ƙungiyoyin farar hula sun maraba da buɗewar, suna kira ga ‘yan gudun hijira su koma gida. Sai dai rahotanni sun ce ana ci gaba da arangama a North Kivu, duk da shirin tsagaita wuta da Angola ta gabatar, wanda aka zargi bangarorin da keta shi.
Rikicin gabashin Congo na ci gaba da haddasa ƙaura da rashin tsaro, yayin da tattaunawar diplomasiyya ke gudana.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














