Tawagar ƙwallon ƙafa ta Cameroon ta sake nuna ƙwarewarta a gasar AFCON, bayan ta kawar da Afirka ta Kudu daga fafatawar zagaye na 16, tare da kakkabe burin Bafana Bafana na kai wa matakin ƙarshe.
Cameroon ta tsallaka zuwa wasan kwata-final na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka bayan ta doke Afirka ta Kudu da ci 2–1 a ranar Lahadi. Junior Tchamadeu ne ya buɗe ƙofar zura kwallo a minti na 34 a filin wasa na Al Medina da ke Rabat, yayin da matashin ɗan wasan Bayer Leverkusen, Christian Kofane, ya ƙara ta biyu bayan mintuna biyu da fara wasa na biyu.
Duk da ƙoƙarin da Afirka ta Kudu ta yi a ƙarshen wasa, inda Evidence Makgopa ya ci ƙwallo ɗaya saura kaɗan a tashi wasan, Cameroon ta tsaya daram har aka tashi. Wannan nasara ta bai wa Indomitable Lions damar fuskantar Morocco mai masaukin baki a kwata-final ranar Juma’a.
Cameroon za ta shiga wasan cikin kwanciyar hankali, ganin cewa duk matsin lamba na kan Morocco, wadda ke neman lashe AFCON karo na farko cikin shekaru 50 a gaban magoya bayanta. Ga Cameroon, kai wa matakin ƙarshe takwas ya zama nasara, musamman bayan rudanin da ya riga gasar, inda shugaban hukumar ƙwallon ƙafarsu Samuel Eto’o ya sallami koci Marc Brys tare da nada David Pagou.
Sabon kocin ya yi nasarar doke Hugo Broos na Afirka ta Kudu, wanda a baya ya jagoranci Cameroon zuwa kofin AFCON a Gabon. Duk da rashin nasarar, Afirka ta Kudu na iya mayar da hankali kan shirin gasar cin kofin duniya, ko da yake sun rasa damar cin kwallo tun da wuri a wasan.
Magoya bayan Cameroon sun yi murnar nasarar da ƙarfi, inda har Eto’o ya halarci wasan, yayin da tawagarsu ta nuna jajircewa wajen kare nasarar har zuwa ƙarshe.













