Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke iyakokin ajiyar kuɗi a bankuna tare da ƙara adadin kuɗin da za a iya cirewa a mako daga N100,000 zuwa N500,000 ga mutum ɗaya. A cikin sanarwar da Dr. Rita Sike ta sanya wa hannu, CBN ta bayyana cewa sabbin dokokin za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026. Sabuwar ka’idar ta tanadi cewa kamfanoni za su iya cire har N5,000,000 a mako, sannan duk wanda ya wuce wannan iyaka za a ci shi tara.
Haka kuma an ayyana cewa na’urar ATM za ta ci gaba da daidaituwa da sabon tsarin, inda mutum zai iya cire N100,000 a rana da N850,000 a mako. CBN ta ce an yi waɗannan sauye-sauyen ne don rage tsadar sarrafa kuɗi, inganta tsaro, da hana safarar kuɗi ta haramtacciyar hanya.












