Kamfanin Dangote Petroleum Refinery ya bayyana cewa yana da cikakken shiri na kammala faɗaɗa ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 a rana zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin wa’adin shekara uku masu zuwa.
Daraktan Gudanarwa na kamfanin, David Bird, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai a harabar matatar da ke Lagos. Ya ce za a aiwatar da aikin ne ta hanyar kwaikwayon tsarin da ke akwai yanzu gaba ɗaya, ba tare da buƙatar sake zane ko sake fasalin injiniya ba.
A cewarsa, wannan tsari zai bai wa kamfanin damar shiga kai tsaye cikin sayo manyan kayan aiki da kuma fara gini. Ya ce an riga an kammala yawancin ayyukan shiri tun kafin fara aikin, lamarin da zai rage lokacin aiwatarwa sosai.
Bird ya bayyana cewa a nan gaba kaɗan, kamfanin zai gudanar da manyan ayyuka biyu a lokaci guda: sayo kayan aikin da ke ɗaukar lokaci mai tsawo, wanda ake sa ran kammala yawancinsu a farkon shekarar 2026, da kuma fara ayyukan gini kamar dasa ginshiƙai da shirya wurin aiki kafin ƙarshen wannan wata.
Ya danganta saurin aiwatar da aikin da hangen nesa na Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, inda ya ce an riga an tanadi fili mai faɗi da aka gyara kuma aka ɗaga tsawonsa domin wannan faɗaɗa tun farko. Hakan, a cewarsa, ya kawar da yawancin jinkirin da ke yawan faruwa a manyan ayyukan masana’antu.
Ya ƙara da cewa kamfanin zai fara aikin tushe a wannan shekarar, kuma ana sa ran fara ganin ginin ƙarfe na fitowa daga ƙasa kafin ƙarshen shekarar.
An fara sanar da shirin faɗaɗa matatar a watan Oktoba, kuma idan aka kammala, zai ƙara ƙarfafa ikon Najeriya wajen tace man fetur a cikin gida, rage dogaro da shigo da mai daga waje, tare da sanya ƙasar cikin manyan ƙasashen da ke fitar da man da aka tace.
Bird ya kammala da cewa kamfanin na da kwarin gwiwar cewa faɗaɗar za ta fara aiki cikin shekara uku, matakin da zai sanya Dangote Refinery cikin manyan matatun mai a duniya.













