Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya miƙa wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, ICP ƙorafi kan shugaban Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, Ahmed Farouk, kan zarginsa da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiya.
A cikin takardar ƙorafin da aka gabatar a ranar 16 ga Disamba, Dangote ya nemi a kama Ahmed, a gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya bisa zarginsa da yin rayuwar ƙarya fiye da ƙarfinsa a matsayin ma’aikacin gwamnati.
A cikin takardar ƙorafin, wadda ofishin Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN) ya samu, Dangote ya zargi shugaban NMDPRA da kashe fiye da dala miliyan bakwai ba tare da wata shaida ta halastacciyar hanyar samun kuɗaɗen shiga ba, har na tsawon shekaru shida kafin a biya kudin makarantar ‘ya’yansa hudu a makarantu daban-daban a Switzerland.
A cikin takardar ƙorafin, Dangote ya ambaci sunayen ‘ya’yan Ahmed guda hudu da makarantunsu da ke Switzerland, ciki har da adadin da aka biya wa kowannensu don tabbatar da zarginsa da kuma neman hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi bincike.
Ya yi zargin cewa Ahmed yana amfani da tsarin NMDPRA don wawure da karkatar da kudaden jama’a don amfanin kai da kuma neman wata manufa ta ƙashin-kai don cutar da al’ummar Nijeriya, lamarin da ya jawo bore da ƙungiyoyi daban-daban suka yi kwanan nan.
Dangote ya yi iƙirarin cewa a tsawon rayuwar shugaban NMDPRA a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati a Nijeriya duka abin da ya samu ko dala miliyan bakwai bai kai ba.
Ɗan kasuwan ya ce ana zargin an karkatar da kuɗin daga asusun gwamnati don biyan kuɗin karatun ‘ya’yansa a ƙasashen waje.
‘Yin abin da ya dace’
“Babu shakka gaskiyar da ke sama game da cin amanar ofis, karya Dokar Ɗa’a ga jami’an gwamnati, azurta kai daga cin hanci da rashawa, da almubazzaranci babban laifi ne na cin hanci da rashawa wanda Hukumarku (ICPC) ta ba da iko bisa doka a ƙarƙashin sashe na 19, na Dokar ICPC don bincike da gurfanarwa,” in ji Dangote.
“Bayan nasarar gurfanar da irin wannan mutumin, a ƙarƙashin sashe na 19 na Dokar ICPC, mutumin zai fuskanci ɗaurin shekaru biyar ba tare da zaɓin tara ba.
“Muna da ƙarfin hali mu bayyana cewa ICPC tana da matsayi mai kyau tare da hukumomin ‘yan’uwanta don gurfanar da laifukan kuɗi da sauran laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa, kuma bayan kafa shari’ar farko, Kotuna ba sa jinkirin hukunta masu laifi.
Dangote ya yi alƙawarin gabatar da hujjoji don tabbatar da zarginsa na wadaƙar da Ahmed ke yi da azurta kansa da cin amanar aikinsa.














