Wasanni

Erik Lamela ya yi ritaya daga ƙwallo bayan kwashe shekara 11 yana fama da ciwon kwankwaso

Tsohon ɗan wasan Tottenham da Argentina, Erik Lamela ya yi ritaya daga ƙwallo bayan ya kwashe shekaru 11 yana fama da ciwon kwankwaso.

Newstimehub

Newstimehub

12 Sep, 2025

afc53408b77896582ebd7cce994d6574b65edff08b5860095a481069726b9d2b main 1

Tsohon ɗan wasan Tottenham ɗan asalin Argentina, Erik Lamela ya bayyana yadda ya kwashe shekaru 11 yana fama da ciwon kwankwaso, har ta kai shi ga ritaya a yanzu.

Lamela ya ce ya kwashe shekara biyar yana shan maganin rage raɗaɗi kullum, kafin a yanzu ciwon ya tilasta masa barin buga ƙwallon ƙafa kacokan.

Ciwon kwankwason nasa ya fara ne sanda yana da shekara 22 amma bayan shekaru 11, yanzu ya ajiye but yana da shekaru 33 a duniya.

A wata tattaunawar bankwana da ya yi mai cike da bayyana gaskiya, ya ce hukuncin yin ritayar ya zo ne saboda fama da ciwon da ya yi tsawon sama da shekaru goma.

Tabarbarewar ciwo