Afirka Siyasa

Eritrea Ta Buƙaci Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Martani Kan Amincewar Isra’ila ga Somaliland

Eritrea ta nemi Kwamitin Tsaron MDD ya dauki mataki kan amincewar Isra’ila ga Somaliland, tana gargadin cewa hakan na iya haddasa hargitsi a yankin da ma duniya baki ɗaya.

Newstimehub

Newstimehub

28 Dec, 2025

guelleh main e1767031986243

Eritrea ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya yi bayyanannen martani game da amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, tana gargaɗin cewa matakin na iya haddasa rashin zaman lafiya a yankin Kahon Afirka da ma duniya baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Eritrea ta fitar ranar Lahadi, ta ce matakin bai zo a bazata ba, face sakamakon shiri da aka daɗe ana yi, wanda ka iya haifar da “matsaloli masu haɗari da hargitsi” ga yankin da tsarin tsaro na duniya. Saboda haka, Eritrea ta nemi Kwamitin Tsaro da mambobinsa su dauki mataki a fili.

Isra’ila ta sanar da amincewarta da Somaliland ranar Jumma’a, lamarin da ya jawo suka daga gwamnatin Somaliya, wasu ƙasashe, da kuma Ƙungiyar Tarayyar Afirka. Ana sa ran Kwamitin Tsaron MDD zai tattauna batun a wani zaman gaggawa ranar Litinin.

Somaliland ta ayyana kanta a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta tun 1991 bayan rugujewar gwamnatin Somaliya, amma Mogadishu da al’ummar ƙasa da ƙasa ba su amince da hakan ba. Eritrea da Somaliya sun maido da huldar diflomasiyya a 2018, kuma tun daga lokacin suka ƙara haɗin gwiwa a fannin tsaro da harkokin yankin.

Majiyar Labari: Trt Hausa