Firayim Ministan Faransa, Sébastien Lecornu, ya ba Ministan Harkokin Ciki Laurent Nunez umarnin fara shirye-shiryen fasaha na yiwuwar zaɓen ‘yan majalisa na gaggawa, idan majalisar dokoki ta kaɗa gwamnati da ƙuri’ar rashin amincewa.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da gwamnati ke fuskantar barazanar ƙuri’ar rashin amincewa guda biyu daga jam’iyyar La France insoumise (LFI) da kuma Rassemblement national (RN). Rahotanni sun nuna cewa Shugaban ƙasa Emmanuel Macron da Firayim Minista sun amince cewa idan gwamnati ta faɗi, za a rushe majalisa.
Idan hakan ta faru, ana sa ran za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisa a ranakun 15 da 22 ga Maris, lokaci guda da zaɓen kananan hukumomi, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan shirye-shiryen gwamnati.
Tashin hankalin siyasar ya samo asali ne daga yarjejeniyar cinikayya tsakanin Tarayyar Turai da Mercosur, wadda ‘yan adawa ke zargin gwamnati da gazawa wajen kare muradun Faransa, musamman a bangaren noma.
Makomar gwamnatin Lecornu na hannun sakamakon ƙuri’ar da za a kaɗa a majalisar dokoki, inda ake buƙatar ƙuri’u 289 domin amincewa da ƙuri’ar rashin amincewa.














