Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fenerbahce da ke buga babbar Gasar Turkiyya ta Super League, Fenerbahce ta raba gari da kocinta Jose Mourinho, kamar yadda ƙungiyar ta sanar a ranar Jumma’a.
“Mun rabu da Jose Mourinho, wanda ya kasance kocin tawagar ƙwallon ƙafarmu tun kakar 2024-2025. Muna godiya da ƙoƙarinsa ga tawagarmu kuma muna masa fatan alheri a aikinsa na gaba,” in ji Fenerbahce a cikin wata sanarwa.
Wannan matakin ya biyo bayan fitar da ƙungiyar daga wasannin share fagen Gasar UEFA Champions League a hannun Benfica, kwanaki biyu da suka gabata.
Mourinho, wanda ɗan Portugal ne da ya yi suna da nasarorin da ya samu a Turai, ya samu nasara sau 37, canjaras sau 14, da kuma rashin nasara sau 11 a wasanni 62 da ya jagoranta a dukkan gasanni tare da Fenerbahce.
Taƙaddama














